Waafir Da Hazaj a Mahangar Ra'i Raba-Gardama

Akwai ra’o’i daban-daban kan yadda ake yanyanka baitocin rubutattun waqoqin Hausa domin fitar da karuruwan da suka dace da ire-iren waqoqin. Masana da manazarta Arulin Hausa na da ra’o’i aqalla guda huxu da suka haxa da mai nasaba da Larabci, wanda M.K.M. Galadanci (1975) ke jagoranta sai kuma mai n...

Full description

Bibliographic Details
Main Author: Ahmadu Bello, mni
Format: Article in Journal/Newspaper
Language:unknown
Published: Zenodo 2023
Subjects:
Online Access:https://doi.org/10.5281/zenodo.8380698
Description
Summary:Akwai ra’o’i daban-daban kan yadda ake yanyanka baitocin rubutattun waqoqin Hausa domin fitar da karuruwan da suka dace da ire-iren waqoqin. Masana da manazarta Arulin Hausa na da ra’o’i aqalla guda huxu da suka haxa da mai nasaba da Larabci, wanda M.K.M. Galadanci (1975) ke jagoranta sai kuma mai nasaba da Tsarin Sautin da ake jinginawa da Junaidu (1981) da kuma mai nasaba da Adabin Baka da ake dangantawa da Muhammad (1973 da 1979 da 1981). Akwai kuma ra’i Raba-Gardama na Bello (2014). An tattauna yadda ake amfani da waxannan ra’o’i inda qafa ta takwas (8) v v – v – da ke samar da karin Kamil da kuma qafa ta shida (6) – – v – mai samar da karin Rajaz kan zo a baitocin waqa xaya, kuma bai kamata su zo a haka ba, tare da yadda za a warware matsalar. Ana iya duba Bello (2014 da 2015 da 2017) domin qarin bayani. Wannan maqalar ta qara qarfafa ra’in Raba-Gardama ta hanyar tabbatar da cewa wannan ra’i na iya yin aiki sosai a kan Waafir da Hazaj, idan qafa ta uku (3) v – v v – da ke samar da karin Waafir ta zo tare da qafa ta biyu (2) v – – – da ke samar da karin Hazaj a baitocin waqa xaya. Ma’ana, kamar yadda qafa ta 8 da ta 6 (8 + 6) ba sa zuwa a gwame wajen samar da kari, haka ma qafa ta 3 da ta 2 (3 + 2) ba sa zuwa. Inda kuma aka sami irin wannan hali a kowace irin rubutacciyar waqa, wannan ra’i na raba-gardama zai fayyace komai qarara ta hanyar qididdigar bayyanar qafa mafi rinjaye, da za a xora karin waqar a kai. An kuma bayyana haka a wasu baitocin waqa guda takwas (8) inda a qarshe aka xora karinsu a Hazaj inda qafa ta biyu v – – – ta zo sau hamsin (50) akasin qafa ta uku v – v v – mai samar da Waafir da ta zo sau talatin (30) kurum.